Akalla Falasdinawa takwas ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, a cewar majiyoyin lafiya da shaidu.
Wata majiyar lafiya ta ce mutane uku ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin saman Isra’ila mara matuki ya kai hari a kusa da makarantar Zeitoun Shahidai a kudu maso gabashin Birnin Gaza.
Wata majiyar lafiya ta sanar da cewa, an kashe ƙarin mutane hudu tare da jikkata wasu da dama a harin da Isra’ila ta kai kan tantunan ‘yan gudun hijira a asibitin shahidan al-Aqsa da ke tsakiyar birnin Deir al-Balah.
Wata majiya ta ce wani harin da Isra’ila ta kai kan wani tanti na ‘yan gudun hijira ya kashe akalla mutum daya a yammacin Khan Younis a kudancin Gaza.
Hukumar tsaron farar hula ta ce, an kuma bayar da rahoton jikkata mutane da dama a wani harin da jirgin sama mara matuki ya kai kan wani wurin sana’ar dinki a wani gida da ke arewacin birnin Gaza.
Hakazalika sojojin Isra’ila sun rushe wasu gine-gine da dama a gabashin birnin Gaza da kuma tsakiyar Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.