Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar a ranar Lahadin nan cewa adadin mutanen da sukayi shahada sanadin hare-haren Isra’ila ya kai 40,972 tun bayan fara yakin wanda ya shiga wata na goma sha biyu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce akalla mutane 33 ne aka kashe a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ta kuma kara da cewa mutane 94,761 ne suka jikkata a zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma jami’an Isra’ila sun ce an kashe fararen hularta uku a wani hari da aka kai kan iyakar Jordan da Gabar Yamma.
Rahotonni sun ce maharin wanda tuni sojojin Isra’ila suka kashe – direban motar dakon kaya ne, wanda ya taso daga Jordan, sannan ya tsaya a shingen binciken ababen hawa ya kuma bude wuta bayan ya sauko daga motar.
Lamarin ya faru ne a yankin da Isra’ila ke iko da shi, kuma nan ne motocin Jordan dauke da kaya ke bi don shiga Gabar Yamma.
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dardar da fargabar barkewar yaki a yankin Gabar ta Tsakiya.
Ko a cikin daren da ya gabata ma an samu musayar hare-haren makamai masu linzami tsakanin Isra’ila da kungiyar Hezbolla ta Lebanon.