Adadin Falasdinawa Da Suka Yi Shahada A Gaza Ya Kai 40,988 Tare Da Jikkatan Wasu 94,825

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan Gaza ya kai mutane 40,988 Ma’aikatar lafiya a Zirin Gaza ta sanar a

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan Gaza ya kai mutane 40,988

Ma’aikatar lafiya a Zirin Gaza ta sanar a jiya Litinin cewa: Hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da kai wa kan Zirin Gaza sun yi sanadin shahadan Falasdinawa 40,988 tare da jikkatan wasu 94,825 tun daga ranar bakwai ga watan Oktoban shekarar bara.

Rahoton kididdiga na yau da kullun ya jaddada cewa: Yawan shahidai da jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon ranaku 339 a Zirin Gaza ya kai matakin aiwatar da kisan kare dangi kan al’ummar Falasdinu. Kamar yadda a baya-bayan nan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aiwatar da kisan kiyashi guda biyu kan iyalai a Zirin Gaza, da ya janyo shahadan Falasdinawa 16 da kuma jikkata wasu 64 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments