Hamas Da Gwamnatin Falasdinawa Sun Yi Allawadai Da Abinda Ke Faruwa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Kungiyar Hamas wacce take fafatawa da sojojin HKI a Gaza, da kuma gwamnatin Falasdinawa a Ramallah duk sun yi allawadai da abinda sojojin HKI suke

Kungiyar Hamas wacce take fafatawa da sojojin HKI a Gaza, da kuma gwamnatin Falasdinawa a Ramallah duk sun yi allawadai da abinda sojojin HKI suke aikatawa a yankin yamma da kogin Jordan a cikin yan makonnin da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shuwagabannin kungiyoyin biyu suka fadar haka a yau Laraba sun kuma bayyana halin da ake ciki a yankin yamma da kogin Jordan yana da hatsari matuka.

Labarin ya kara da cewa a safiyar yau Laraba kadai sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 11 a wurare daban daban a yankin, musamman daga arewaci.

Sojojin HKI suna amfani da jiragen wadanda ake sarrafasu daga nesa saboda kai hare hare a kan falasdinawa a kan garuruwa daban daban a yankin yamma da kogin Jordan. Sannan suna amfani da tankunan yaki da kuma sojoji a kasashe don murkushe boren Falasdinawa a yankin.

Sojojin suna shiga gida gida a wasu yankuna suna kashe matasa Falasdinawa, wadanda suke nuna turrjiya ga sojojin yahudawan wanda suke son korar Falasdinawa daga yankin.

Kimani kwanaki 330 kenan da fara yaki a gaza, sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa a gaza kadai kimani dubu 40 a yayinda wasu dubu 92 kuma suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments