Hamas: Kalaman Biden Na Karfafa Gwiwar Isra’ila Wajen Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da ikirarin shugaban Amurka Joe Biden na cewa kungiyar tana ja da baya daga yarjejeniyar tsagaita

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da ikirarin shugaban Amurka Joe Biden na cewa kungiyar tana ja da baya daga yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Isra’ila kan Gaza, tana mai kiran kalaman nasa a matsayin bayar da lasisi ga Isra’ila ta ci gaba da yakin kisan kare dangi a yankin Gaza da ta  yi wa kawanya.

Hamas ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan  Talata, bayan da Biden ya zargi da dakile  yarjejeniya da zata kai Isra’ila ga dakatar da yakin da take yi a Gaza .

Ikirarin nasa bai dace ba, ba ya nuna hakikanin matsayin kungiyar, wanda ke da sha’awar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta”, in ji Hamas, tare da bayyana cewa wadannan kalamai na ba wa gwamnatin Isra’ila damar yin karin laifuffuka kan fararen hula Falasdinawan da ba su da kariya.

Kungiyar  ta kuma jaddada cewa ta amince da shawarar tsagaita bude wuta da shugaban Amurka ya gabatar a watan Yuni. Sai dai ya ce, sabuwar shawara da Amurka da Isra’ila suka gabatar ta hada da sabbin tanade-tanade da suka saba wa tsarin da aka gabatar a baya.

Hamas ta kuma kara da cewa sabbin sauye-sauyen da Amurka ta yi kan kudurin na nuni ne da karkata kai tsaye ga Isra’ila da kuma yadda Washington ke da hannu a yakin kisan kare dangi a kan fararen hula marasa kariya a zirin Gaza.”

Har ila yau, ta bayyana sauye-sauyen na baya-bayan nan a matsayin yin fatali ne ga tsarin da ya gabata, tare da zargin Washington da mika wuya ga sharuddan da gwamnatin Isra’ila ta gindaya.

Hamas ta kara jaddada cewa Firaministan Isra’ila Netanyahu shi ne “kodayaushe ke kawo cikas ga yarjejeniya tare da kafa sabbin sharudda da wasu bukatu,” bayanin ya kira Amurka da “ta sauya manufarta na nuna son kai ga ‘yan sahayoniya masu aikata laifukan yaki.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments