Iran: Yar Wasan Tekwando Wacce Ta Sami Lambar Azurfa Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Wasa Don Daukaka Iran

Yar wasan tekwando wacce ta sami lambar yabo da azurfa a wasannin Olympic na shekara ta 2024 da aka kammala a birnin Paris na kasar

Yar wasan tekwando wacce ta sami lambar yabo da azurfa a wasannin Olympic na shekara ta 2024 da aka kammala a birnin Paris na kasar Faransa a cikin wannan ta sha alawashin ci gaba da wasa don daukaka kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya nakalto Mino Nimat-Zade tana fadar haka a wata hira ta musamman da wakilin Parstoday bayan ta dawo gida daga kasar Faransa.

Mino diyar shekara 19 a duniya ta sami nasara a zagaye na farko a kan abokin hamayyarta sannan a zagaye na biyu a wasan Olympic bangaren mata a birnin Paris, wanda ya bata damar samun lamabar Azurfa a karshen wasar.

Mino ta godewa mai horar da ita Mehruuz Sa’ii a kan horas da ita wanda ya kaiga ta sami lambar yabo ta azurfa.

Iran ce ta zo kashe na 21 a yawan lambobin yabo a gasar na Olympic tare da samun lambobib yabo har 11 wadanda suka hada da zinari da Azurfa da kuma Takunza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments