Iran Ta Musanta Zargin Amurka Na Shihsigi A Cikin Harkokin Zaben Kasar Na Wannan Shekara

Jakadan kasar Iran a MDD ya musanta zargin da wasu hukumomi a kasar Amurka suka yiwa kasar na shishigi cikin al-amuran zaben shugaban kasa wanda

Jakadan kasar Iran a MDD ya musanta zargin da wasu hukumomi a kasar Amurka suka yiwa kasar na shishigi cikin al-amuran zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a kasar a cikin watan Nuwamba na wannan shekara ta 2024.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Amir Saeid Iravani Jakadan JMI a MDD yana fadar haka ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Iran bata da wani amfani da zata samu a kutsawa cikin al-amuran zaben shugaban kasar na Amurka.

Kafin haka dai wasu hukumomin tsaro na kasar Amurka wadanda suka hada da hukumar FBI sun bada sanarwan hadin giuwa inda suka zargi JMI da shishigi cikin al-amuran zaben shugaban kasa na kasar ta Amurka, ta hanyar kutsawa cikin shafukan yanar gizo na yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun Democrats da kuma Republican gaba daya.

Iravani ya kara da cewa idan gwamnatin kasar Amurka tana da gaskiya dangane da wannan zargin, to tana iya gabatar da shaida ko shaidu hakan ga MDD.

Kafin haka wasu hukukomin kasar ta Amurka sun zargi kasar Iran da kutsawa cikin shafin Microsoft a kwanakin baya, wanda ya rikata harkokin da dama a duniya, daga ciki hard a na bankuna, tashoshin jiragen kasa da na sama da sauranu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments