MDD : Fadada Matsugunan Isra’ila A Yammacin Kogin Jordan Ya Saba Wa Dokokin Kasa Da Kasa

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta dangane da fadada matsugunan da Isra’ila ke yi a baya-bayan nan da kuma sauye-sauyen da shari’a ta tanadar a

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta dangane da fadada matsugunan da Isra’ila ke yi a baya-bayan nan da kuma sauye-sauyen da shari’a ta tanadar a yankin yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye.

A cewar MDD wadannan ayyuka sun saba wa dokokin kasa da kasa, ciki har da hukuncin da kotun kasa da kasa ta (ICJ) ta yanke a watan Yulin da ya gabata.

A wata sanarwa da ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar jiya litinin ya ce matsugunan da basa bisa doka, da tashe-tashen hankulan da yahudawa masu tsautsauran ra’ayi ke aikatawa ga mazauna yankin su ne ummul aba’isin tauye hakkin bil’adama a yammacin kogin Jordan, ciki har da gabashin birnin Kudus.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, kwanan nan da aka sanar da gina sabbin matsugunai a yankin Nehaletsel da ke yammacin birnin Bethlehem, yana matukar barazana ga rayuwa, tsaro da kuma zirga-zirgar Falasdinawan da ke zaune a kauyuka biyar da ke makwabtaka da ita, tare da yin babbar barazana ga ci gaba da wanzuwar kasar Falasdinu.

A karkashin dokokin kasa da kasa, ana daukar duk matsugunan Yahudawa a yankunan da aka mamaye a matsayin haramtattu.

A shekarar 1967 ne gwamnatin Isra’ila ta mamaye birnin Kudus inda ta ci gaba da gina manyan matsugunan Yahudawa a birnin.

Tun bayan mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa gabar yammacin kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus a shekara ta 1967, an gina matsugunan Yahudawa sama da 250 a wadannan yankuna, inda mutane kusan 700,000 ke zaune.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments