Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito gangami a birnin San’a babban birnin kasar da kuma sauran jihohi don nuna goyon bayansu, kamar yadda suka saba a duk jumma’a ga al-ummar Falasdinu a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a birnin San’aa babban birnin kasar dubban daruruwan Yemenawa sun taru a danganen 70 a tsakiyar birnin inda suka yi allawadai da ci gaba da kissan kare dangin da sojojin HKI suke yi a Gaza.
Sun kuma kara da cewa zasu ci gaba da kasancewa tare da Falasdinawa har zuwa lokacinda HKI zata kawo karshen yaki a Gaza.
Gangamin Yemenawan ya jinjinawa sojojin kasar wadanda suka kai hari da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa a cikin tsakiyar birnin Te-Aviv babban birnin HKI.
A wani labarin kuma sojojin kasar ta Yemen sun bada labarin cilla makamai masum linzami kan wasu jiragen ruwa a tekun Maliya saboda sabawa dokar hana dukkanin jiragen wadanda suke zuwa HKI wucewa ta tekun.