A safiyar yau ce shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya kare majalisar ministocinsa mai mambobi 19 a gaban majalisar dokokin kasar ya kuma bayyana cewa su na da korewar da ya dace su rike wadannan makaman da ya basu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bisa doka ta 202 na kundin tsarin mulkin JMI dai shugaban yakamata ya gabatar da sunayen ministocinsa a gaban majalisar dokokin kasar don tantancewa cikin makonni biyu kacal da kama aiki a matsayin shugaban kasa.
Daga cikin sunayen da shugaban ya bada tarihin rayuwar ko wanne daga cikinsu da kuma takardun karatunsa.
Daga cikin fitattun yan siyasa wadanda shugaban ya gabatar har da Abbas Araqchi a matsayin ministan harkokin waje, da Himmati tsohon gwamnan babban bankin kasar a matsayin ministan tattalin arziki.