Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Ce A Kowace Rana Ana Kashe Falasdinawa 130 A Gaza

Babban jami’in Hukumar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce: A Kowace rana sojojin mamaya suna kashe rayukan Falasdinawa 130 a Zirin

Babban jami’in Hukumar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce: A Kowace rana sojojin mamaya suna kashe rayukan Falasdinawa 130 a Zirin Gaza

Volker Turk, babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: A yau yana wakiltar wani mummunan ci gaba ga duniya, yayin da aka tabbatar da hasarar rayukan Falasdinawa 40,000 a hukumance, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Kuma bayanin da ya fito daga ofishin sakamakon adadin wadanda suka mutu ya kai wannan yawan mutanen, sannan yawancin wadanda suka mutun Mata da kananan yara ne.

Volker ya ce, wannan lamarin da ba za a iya tunaninsa ba, ya samo asali ne sakamakon gazawar da sojojin mamaya haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi ne na ci gaba da bin ka’idojin yaki da kiyaye dokokin kasa da kasa.

Sanarwar da babban jami’in ya fitar ta ce, kimanin mutane 130 ne ake kashewa a kowace rana a Gaza a tsawon watanni goma da suka gabata, baya ga rushe-rushen gidaje da cibiyoyin lafiya da makarantu da kuma wuraren ibadu da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi, lamarin da ke da ban tsoro matuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments