Jiragen yakin Amurka da kuma Burtaniya sun kai hare hare kan wani yanki a yammacin lardin Hudaida na kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hare haren na jiya dai an kaisu ne a garin As-salif na lardin Hudaida amma har yanzun babu labarin irin barnan da suka yi a garin. Lardin Hudaida na bakin tekun Maliya ko Red Sea dai shi ne yanki mafi yawan mutane na biyu a kasar ta Yemen.
Gwamnatocin kasashen Amurka da Burtaniya suna kokarin hana kasar Yemen aiwatar da dokar da ta kafa ta hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Maliya saboda taimakawa mutanen Gaza wadanda sojojin HKI suke kashewa tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.
Ya zuwa yanzun kuma kasar ta Yemen ta sami nasarori masu yawa a tabbatar da dokar duk tare da hare haren da kasashen Amurka da Burtaniya suke kai mata don tilasta mata dakatar da ita.