Imam Khamina’i Ya Bukaci A Fuskanci Makiya Da Kaifin Hankali A Yakin Dabarbarun Da Ake Fafatawa Da Makiya A Halin Yanzu

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khamina’i ya karfafa bukatar a fuskanci makiya a yakin dabarbaru ko cacan baki, wanda

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khamina’i ya karfafa bukatar a fuskanci makiya a yakin dabarbaru ko cacan baki, wanda ya hada da tsoratarwa da karfi soje wanda makiya suke amfani da su a halin yanzu, don musulmi su ji tsoro su jada baya. Ya kara da cewa duk wata jada baya da musulmi zasu yi saboda tsoro, to wannan yana iya jawo fushin All.. a kan musulmi. Sai dai idan jada bayar na daga cikin dabarbarun yaki, inji jagoran.

Ya kuma bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da iyalan shahidar daga lardin Kahkiloye –Buwir-Ahmad a gidansa a nan Tehran, ya ce tsoratar da mutane ko musulmi da girman makiya wanda wasu suke yi yana daga cikin irin wannan yakin na dabarbaru, wanda bai kamata musulmi su tsorata ba.

Sayyid Khamina’i ya kara da cewa shahidammu sun sami nasara a wannan fagen kuma sun karya makiya da wadannan dabarbarun. Ya kuma kara da cewa Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI a ko yaushe yakan sanya Imani da dogaro da All..da kuma yin abinda ya zama wajibi ga musulmi ya yi, ba tare da jin tsaro ko fargaba ban  makiya ba.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments