JMI ce kasa ta farko a cikin kasashen Musulmi a samar da ilmin fasahar Quantum
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa JMI ce kasa ta farko a samar da sabbin ilmi a fasahar Quantum a cikin kasashen musulmi sannan itace ta 8 a duniya.
Shafin yanar gizo na ‘Web of Science’ ya tabbatar da hakan ya kuma kara da cewa nan gaba JMI zata iya zama cikin kasashe yan kadan a duniya a fannin ci gaba na fasahar Quantum.
An fara samar da fasahar quantum ce a farkon karni na 20 miladiyya, kuma da wannan fasahar ce aka samar da abinda ake kira ‘Transistor’ a karon farko a duniya. Sannan daga nan aka sami sauyi da ci gaba mai yawa a fasahar ilmin lissafi ko ‘Physics’ wanda ya kaiga samar da kumfuta da kuma ‘internet’ daga baya.
Kasar Iran, duk tare da takunkuman tattalin arzikin kasashen yamma masu tsanani a kanta, ta shiga gasar samar da fasahar quantum da sauran kasashen duniya, kuma ta sami ci gaban a zo a gani a wannan fannin.
Kamfanin dillancin labarai na Parstoday ya nakalto Sayyid Ahmad Fazil-Zade shugaban cibiyar raya fasahar da ilmi na kasashen musulmi (ISC) yana cewa: Iran ta sami ci gaba a dukkan fannonin ilmin quabtun a duniya, kuma ita ce mai matsayi na 8 a kasashen duniya a halin yanzu. Sannan akwai fatan a cikin shekaru 20 masu zuwa kasar zata kai matsayi mafi kyau a fasahar quantum da kuma fannin ilmin lissafi.