Sojojin Mamayar Amurka Sun Kai Hare-Hare Kan Kauyuka Da Garuruwan Kasar Siriya

Rundunar sojin Amurka ta kai hare-hare kan garuruwa da kauyuka a yankin Deir ez-Zor da ke gabashin kasar Siriya Sojojin mamayar Amurka sun kaddamar da

Rundunar sojin Amurka ta kai hare-hare kan garuruwa da kauyuka a yankin Deir ez-Zor da ke gabashin kasar Siriya

Sojojin mamayar Amurka sun kaddamar da wasu jerin kazaman hare-haren wuce gona da iri a cikin daren jiya wayewar garin yau Laraba kan kauyuka da garuruwa da suke yankin Deir ez-Zor da ke gabashin kasar Siriya, da suka bayyana a matsayin mayar da martani kan hare-haren da ake kai musu ba bisa ka’ida ba a sansanoninsu da suke cibiyar iskar gas na “Koniko” da ke gabashin kasar ta Siriya.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya watsa rahoton cewa: Sojojin mamayar Amurka sun kaddamar da wasu hare-hare kan wurarem dakarun da ke goyon bayan sojojin Siriya da suke kauyuka da garuruwan Khasham. Marat da Hawija Sukr da suke yankin arewa maso gabashin kasar a lardin Deir ez-Zor ta hanyar yin amfani da manyan bindigogi da jiragen sama marasa matuka ciki.

A halin da ake ciki dai, sararin samaniyar yankin na ganin tsananin tashin jiragen saman yakin Amurka, sannan har ya zuwa yanzu, babu wani bayani kan irin barnar da hare-haren na Amurka suka janyo a kan wadannan kauyuka da garuruwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments