Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ta Umarci Dabban Falasdinawa Su Fice Da Muhallinsu

Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta umurci Falasdinawa 100,000 ‘yan gudun hijira da su fice daga garin Hamad nan take Majiyar gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar

Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta umurci Falasdinawa 100,000 ‘yan gudun hijira da su fice daga garin Hamad nan take

Majiyar gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Sojojin mamaya sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga yankunan da ke birnin Khan Yunus da ke kudancin Zirin Gaza ba tare da la’akarin abin da zai biyo bayanficewar ba.

Wakilin gidan talabijin na Al-Alam da ke Deir al-Balah ya rawaito cewa: Sojojin mamayar sun bukaci Falasdinawa ‘yan gudun hijira da mazauna unguwar Al-Jalaa da aka fi sani da garin Hamad da ke arewacin birnin Khan Yunus, da su fice daga garin nan take, yayin mutane sama da 100,000 ne a tsakanin wadanda suka rasa matsugunansu suke garin.

A lokaci guda kuma, jiragen saman yakin sojojin mamayar suka ci gaba da yin ruwan bama-bamai kan yankunan birnin Khan Yunus.

Yawan mutanen da suka rasa matsugunansu daga gabashi da tsakiyar Khan Yunus an kiyasta cewa sun zarce Falasdinawa 70,000, sannan jiragen saman yakin sojojin mamayar sun yi ruwan bama-bamai a yankunan Al-Qarara, Al-Jalaa, Khuza’a, Bani Suhaila, da hasumiyar Hamad lamarin da ya kai ga rugujewar manyan yankunan gaba daya.

Wannan dai shi ne karo na uku a cikin kimanin mako guda da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka sanar da aniyarsu ta ficewa daga birnin Khan Yunus, sannan a halin yanzu suka sake sanar da fara wani sabon farmakin soji a cikinsa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments