Osama Hamdan: Dole ne Amurka ta daina goyon bayan Isra’ila 

Babban kusa a kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya bayyana cewa, Isra’ila ba ta da niyyar kawo karshen yakin da take yi da al’ummar Gaza.

Babban kusa a kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya bayyana cewa, Isra’ila ba ta da niyyar kawo karshen yakin da take yi da al’ummar Gaza.

Osama Hamdan, wanda mamba ne ofishin siyasar kungiyar ya ce, Amurka ce kawai za ta tilasta Isra’ila ta daina kisan jama’a a Gaza idan har tana da niyyar yin hakan.

Ya kara da cewa “Idan masu shiga tsakani na son kawo karshen cin zarafin Isra’ila a Gaza, dole ne Amurka ta daina tallafa mata a wannan yaki a dukkanin banagarori.”

Hamdan ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da tashar Al-Manar ta kasar Lebanon a daren jiya.

“Matsayinmu a bayyane yake, kuma ba ma jiran tattaunawa kan wata sabuwar matsaya,” in ji shi, yayin da yake magana kan tattaunawar da ake yi tsakanin masu shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Ya kara da cewa, “Akwai wata takarda da muka amince da ita, kuma muna jiran sanarwa kan hanyoyin aiwatar da abubuwan da ta kunsa, wadanda suka hada da dakatar da wuce gona da iri, da janyewar sojojin yahudawa daga Gaza, da taimaka wa Falastinawa da aka raba da muhallansu, da kaddamar da sake gina yankin zirin Gaza ” in ji shi.

Rahotanni sun ce Hamas ta amince da kudirin Masar da Qatar, wanda ya hada da tsagaita bude wuta, da janyewar sojojin Isra’ila gaba daya daga Gaza, da musayar fursunoni, da sake gina yankin, da kuma janye shingen da Isra’ila ta kafa.

Sai dai Isra’ila ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, inda Benjamin Netanyahu ya ce janyewar sojojin mamaya daga zirin Gaza “zai bar kungiyar Hamas ta ci gaba da iko da yankin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments