Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Ce Daukar Fansar Shahid Fuad Shukr Ya Zama Dole A Cikin Yan Kwanaki Masu Zuwa

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan nasarallah ya bayyana cewa daukar fansar jinin shahid Fuad Shukr daya daga cikin manya manyan kwamandojin kungiyar

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan nasarallah ya bayyana cewa daukar fansar jinin shahid Fuad Shukr daya daga cikin manya manyan kwamandojin kungiyar wanda jirginn yakin HKI ya kashe a yankin Dahiya Junibiyya na birnin Berut ya zama wajibi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyid Nasarallah yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a Jiya Talata a birnin Beirut, sannan ya kara da cewa daukar fansar,  mai yuwa ya zo tare da na sauran kawancin kasashe da kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin, ko kuma a daddaikunsu.

A wani wuri a cikin jawabinsa Sayyid Nasarallah ya bukaci saurann kasashen Larabawa su fuskanci hatsarin da ke tattare da HKI, don bai kamata su zama kamar jimina ba, su binne kansu a kasa don kada su ga hatsarin da ke gabansu.

Shugaban ya ce HKI ba ta da jan layi, idan ta sami dama ba zata bar kowa ba, ko da kuwa wadanda suke ganin suna kawance da ita ne a yanzu, don tana da agenta ta mamayar kasashen larabawa a yankin gaba daya.

 Daga karshe Sayyid Nasarrah yace jinkirin da kungiyar ko kawancen kungiyar suka yi na maida martani kan HKI dangane da kashe-kashen Beirut da Tehran, shi ma bangaren ne na ukubar kissan wadannan shuwagabanni masu gwagwarmaya da HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments