Babban sakataren kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah ya ce fada ya shiga wani sabon yanayi bayan da Isra’ila ta kashe babban kwamandan dakarun Hizbullah Fouad Shukr, da shugaban Hamas Ismail Haniyeh.
A wani jawabi da aka watsa kai a wurin jana’izar Shukr a ranar alhamis, shugaban kungiyar Hizbullah ya ce Isra’ila ta wuce dukkanin iyakoki ta hanyar aiwatar da wannan kisan gilla, kuma dole ne ta yi tsammanin “fushi da daukar fansa daga dukkan bangarorin da ke goyon bayan Gaza.”
Sayyid Nasrallah ya ce ya umarci dakarun kungiyar Hizbullah da ke kudancin kasar Lebanon da su dakatar da ayyukansu a ranakun Laraba da Alhamis amma za su ci gaba da aiki da karfi a yau Juma’a.
Kasashe da dama sun nemi kungiyar Hizbullah da ta mayar da martani ta hanyar da ba zata janyo barkewar yaki ba, kamar yadda kuma wasu suke kiran kungiyar da ta kai zuciya nesa.
Yace: “Babu wata tattaunawa kan wannan batu. Abin da kawai ke tsakaninmu da ku shi ne ranaku, darare da fagen fama,” Nasrallah ya kara da cewa: “Tabbas za mu mayar da martani mai matukar muni a kan Isra’ila, Wannan shine karshen Magana kan hakan.”
Sayyid Nasrallah ya nanata cewa, ba kungiyar Hizbullah ba ce ke da hannu a harin makamin roka da aka kai a garin Majdal Shams da ke tuddan Golan na kasar Syria da Isra’ila ta mamaye a ranar Asabar, inda aka kashe yara 12.
Ya ce Isra’ila ta kai harin na roka ne da gangan domin samun hujjar kashe kwamandojin ‘yan gwagwarmaya.