An binne gawar Isma’il Haniyya a birnin Doha na Qatar

An yi jana’izar Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas, a babban birnin Qatar Doha, taron janazar da ya samu halartar manyan

An yi jana’izar Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas, a babban birnin Qatar Doha, taron janazar da ya samu halartar manyan jami’ai daga sassan yankin.

An binne gawar Haniyeh da aka nannade da tutocin Falasdinu a makabartar masarautar kasar  da ke Lusail a arewacin Doha, Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad-Reza Aref da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Ali Baqeri Kani da sauran manyan baki da wakilai daga bangarorin Palasdinawa. .

Kafin haka dai, dubban masu zaman makoki da suka hada da wakilan kasashen duniya da dama sun gudanar da sallar jana’izar a babban masallacin birnin Doha, masallacin Imam Muhammad bin Abdul Wahhab, cikin tsauraran matakan tsaro.

An gudanar da addu’o’i da zanga-zangar yin Allawadai kisan  shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Gaza da yammacin kogin Jordan, tare da wasu kasashe da dama da suka hada da Jordan, Lebanon, Turkiyya, Yemen, Pakistan, Malaysia, da Indonesia Irakim Morocco, Tnunisia, Aljeriya da dai sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments