Iran: Ma’aikatan Leken Asiri Na Kasar Iran Wargaza Shirye Shiryen Yan Ta’adda Har Sau 79

Ma’aikatar leken asiri na kasar Iran ta bada rahoton cewa daga ranar 21 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Yunin shekara ta 2024,  ta

Ma’aikatar leken asiri na kasar Iran ta bada rahoton cewa daga ranar 21 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Yunin shekara ta 2024,  ta sami nasarar wargaza shirye shiryen yan ta’adda na kai hare hare a wurare da dama a cikin kasar har sau 79.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto sashen yaki da ta’addanci na ma’aikatar yana fadar haka a wani rahoton da ya fitar a yau Asabar. Ya kuma kara da cewa, a fafatawa da yan ta’adda da masu taimaka masu a cikin kasar, a cikin wadannan kwanaki, ya sa sun kama yan ta’adda da dama, sun kuma kwace makamai na yaki har na’i 560 daga hannunsu, da albarusai dubu 42, da kuma boma bomai 9 wadanda aka dana su a wasu wurare a cikin kasar, suna jiran lokacin tashinsu kawai, sai jami’an ma’aikatar suka sami nasarar kwancesu.

Rahoton ya kara da cewa wadannan yan ta’adda sun shigo kasar ne ta kan iyakokin kasar na gabas amma suka fada cikin tarkon jami’ab ma’aikatar, inda suka halaka da dama daga cikinsu a yayinda wasu kuma aka kamasu da ransu.

Daga karshen rahoton ya kammala da cewa labarai masu muhimmanci da suka samu daga wani tsohon dan ta’adda mai suna Abdullahi Kuwaiteh, ya basu damar gano asirai da kuma kama wasu yan ta’adda masu yawa a cikin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments