Pezeshkian: China, Rasha sun tsaya tare da mu, dole ne Amurka ta dauki darasi

Zababben shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya fitar da wani rubutaccen sako da ke bayyana ra’ayinsa, mai taken “Sakona zuwa ga sabuwar duniya.”

Zababben shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya fitar da wani rubutaccen sako da ke bayyana ra’ayinsa, mai taken “Sakona zuwa ga sabuwar duniya.”

Pezeshkian na shirin zama shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran a hukumance na 9, tare da gudanar da bikin rantsar da shi a majalisar dokokin kasar da aka fi sani da Majlis a ranar 30 ga watan Yulin 2024.

An buga sakon ne a jaridar Tehran Times, inda ya bude sakon nasa ne ta hanyar tabo batun zaman lafiyar kasar Iran na musamman a yanayin da ake ciki a yankin, inda ya ce an gudanar da zabe cikin tsari da lumana.

Wannan kwanciyar hankali, da kuma yadda aka gudanar da zabuka cikin tsafta, na nuna irin fahimtar da Jagora Ayatullah Khamenei yake da ita ne, da sadaukarwar da al’ummar kasar Iran  suka yi wajen kare mulki na dimokuradiyya ko da a cikin mawuyacin hali.”

Ya jaddada cewa ya yi takara a kan wani dandali da ya shafi kawo sauyi, hadin kan kasa, da kyakkyawar hulda da duniya, inda a karshe ya samu amincewar ‘yan kasarsa a akwatin zabe, musamman matasa mata da maza. Ya bayyana cewa “yana matukar mutunta amanar da suka doras a wuyansa,  kuma zai jajirce wajen kare ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments