NBS: An Samu Karuwar Ayyukan Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ce dai ta fitar da alƙaluma cewa ‘yan Najeriya sun bai wa jami’an gwamnatin ƙasar naira biliyan 721 kwatankwacin dala

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ce dai ta fitar da alƙaluma cewa ‘yan Najeriya sun bai wa jami’an gwamnatin ƙasar naira biliyan 721 kwatankwacin dala biliyan 1.26 a matsayin cin hanci a 2023.

Rahoton ya ce ƴan Najeriyar sun bayar da rashawa sau miliyan 87, amma adadin ya yi ƙasa idan aka kwatanta da miliyan 117 da suka bayar a 2019.

Cikin duka ƴan Najeriyan da suka ga aƙalla wani jami’in gwamnati ɗaya cikin wata 12 kafin gudanar da binciken a 2023, kashi 27 sun bai wa jami’in cin-hanci.

Idan aka kwatanta da abin da aka saba gani a baya, hakan na nufin yawan biyan cin-hanci a Najeriya ya ragu kaɗan zuwa kashi 23 tun daga 2019, lokacin da aka samu kashi 29 da suka bayar da cin hanci.

A wuraren da kuma aka tambayi cin-hanci amma mutane suka ƙi bayarwa, an ba da cin-hancin fiye da sau ɗaya cikin haɗuwa uku (kashi 34 cikin 100) a 2023.

Sai dai kuma kashi 70 cikin 100 na mutanen da aka nemi su bayar da cin hancin a 2023 sun ƙi bayarwa sama da sau ɗaya.

Kazalika, binciken ya gano cewa raguwar bayar da cin-hancin ta fi yawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya da kashi 76, duk da cewa sauran yankunan sun samu sama da kashi 60 cikin 100.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments