Nasrallah : Ba Ma Fargabar Shiga Yaki Da Isra’ila

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Lebanon ta Hezbollah, Hassan Nasrallah, ya yi alkawarin daukar fansa mai tsanani idan har Isra’ila ta yunkuri mamaye kasar ta Lebanon.

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Lebanon ta Hezbollah, Hassan Nasrallah, ya yi alkawarin daukar fansa mai tsanani idan har Isra’ila ta yunkuri mamaye kasar ta Lebanon.

Nasrallah ya bayyana a yayin wani taron tunawa da wani kwamandan kungiyar Muhammad da aka yi a Beirut, cewa: “dakarun kungiyar ba su san tsoron yaki ba.

Dangane da barazanar da jami’an Isra’ila suka yi na kaddamar da yaki kan kasar Labanon, Sayyid Nasrallah ya ce: Mun ji kalamai daga Ministan Yakin Isra’ila Yoav Gallant na cewa idan yakin Gaza ya tsaya, ba lallai ba ne a tsaya a Lebanon.

Muna gaya masa, idan makiya suka far wa kudu, za mu kare kanmu’’

Babban jami’in Hizbullah ya ce ‘yan kasar Labanon sun yi nasarar dakile yadda makiya suke yakar Gaza, yana mai tabbatar da cewa yankunan da aka mamaye na arewa suna da alaka da Gaza, kuma domin samun kwanciyar hankali a arewacin kasar, “dole ne a daina yakin Gaza.”

Nasrallah ya ce, “Idan da makiya sun samu nasara cikin gaggawa a Gaza, da Lebanon ta kasance farkon wanda zasu yi ma barazana.”

Shugaban kungiyar Hizbullah ya jaddada gazawar gwamnatin Isra’ila wajen cimma manufofinta a Gaza.

Nasrallah ya ce, dagewar da Benjamin Netanyahu ya yi kan hare-haren na Rafah, wata alama ce da ke nuna gazawar Isra’ila wajen cimma manufofinta.

Isra’ila ta yi ikirarin cewa farmakin na Rafah zai dauki “makonni biyu” amma “ya kwashe watanni biyu da kwanaki hudu, mai yiwuwa ma ya tsawaita zuwa watanni hudu,” in ji Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments