Yawan Man Da Iran Ke Hakowa Ko Wace Rana Ya Karu Daga Miliyan 2,2 Zuwa 3,6

Ministan mai na Iran ya bayyana cewa yawan man da kasar ke hakowa a kowace rana ya kai ganga miliyan 3.6 daga ganga miliyan 2.2.

Ministan mai na Iran ya bayyana cewa yawan man da kasar ke hakowa a kowace rana ya kai ganga miliyan 3.6 daga ganga miliyan 2.2.

Javad Owji ya shaidawa manema labarai cewa, duk ganga 100 na man da ake hakowa yana kawo wa Iran kudaden shiga da ya kai dalar Amurka biliyan 2.8 a duk shekara, yana mai cewa masana’antar mai ta kasar ta yi nasarar kai gangar mai zuwa ganga miliyan 3.6 a kowace rana.

Mista Owji ya kara da cewa idan aka kara yawan man da ake hakowa da kuma inganta karfin matatar, hakan zai kara samun kudaden shiga wa kasar daga kasashen waje.

Ministan mai na Iran ya ce ana shirin samar da ganga miliyan 4 na mai a kowace rana ya zuwa watannin masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments