Hizbullah Ta Bayyana Shahid Nasser A Matsayin Mutum Mai Sadaukarwa A Tafarkin Jihadi

Sashen yada labarai na rundunar Hezbollah ta Hezbollah ta fitar bayani da a cikinsa yake bayyana shahid Mohammad Nehme Nasser, “Hajj Abu Nehme,” a matsayin

Sashen yada labarai na rundunar Hezbollah ta Hezbollah ta fitar bayani da a cikinsa yake bayyana shahid Mohammad Nehme Nasser, “Hajj Abu Nehme,” a matsayin wani jajirtaccen mutum mai sadaukarwa a tafarkin jihadi da gwagwarmaya.

Haka nan kuma kungiyar ta fitar da takaitaccen tarihin rayuwarsa.

An haife shi a ranar 6 ga Mayu, 1965, a garin Hadatha da ke kudancin kasar Lebanon, shahid Nasser yana daga cikin mayaka na farko da suka shiga kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon, a lokacin da ya shiga sahun mayaka a shekarar 1986 a lokacin yana da shekaru 20 a duniya.

Ya taka rawa a wasu hare-hare, a wani bangare na fafutukar ‘yantar da garuruwa da kauyukan Lebanon daga hannun sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila.

A daya daga cikin irin wannan samame, Hajj Abu Nehme na daya daga cikin mayaka da dama da suka jagoranci kutsawa cikin sansanin sojojin Isra’ila a Beit Yahoun, wani kauye da ke makwabtaka da Hadatha kusa da Benit Jbeil a kudancin kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments