Sigrid Kaag: Ayyukan Agaji Na Fuskantar Babban Cikas A Gaza Sakamakon Hare-Haren Isra’ila

A wani rahoto da babbar jami’iar Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta bayyana cewa, ayyukan gaji a sassa na yankunan zirin Gaza na fuskantar babbar

A wani rahoto da babbar jami’iar Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta bayyana cewa, ayyukan gaji a sassa na yankunan zirin Gaza na fuskantar babbar matsala,  kuma kai kayayyakin ya yi ragu matuka tun daga ranar da  Isra’ila ta kaddamar da harin soji a kudancin birnin Rafah ranar 6 ga Mayun da ya gabata.

Sama da al’ummar Gaza miliyan 1.9 daga cikin miliyan 2.3 daga cikin mutane miliya 2.4 da suke rayuwa a yankin sun tagayyara, kamar yadda Sigrid Kaag ta faɗa wa Kwamitin Tsaro na MDD.

Ta ce harkar lafiya ta ruguje, an rusa makarantu, kuma zafin yanayi yana karuwa, ga kuma karancin ruwan sha da tsaftar muhalli, “hadarin ɓarkewar cututtuka masu yaduwa yana karuwa.”

“Babu wani zabi day a wuce kawo karshen wannan kisan bil adama da shawo kan lamarin ta hanyar siyasa, da girmama dokokin kare dan-adam, musamman kare farar hula, da samar da kyakkyawan yanayi don rarraba kayan agaji,” cewar Kaag, babbar jami’ar MDD kan agaji da sake gina Gaza da Isra’ila ta daidaita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments