Yakin Da Ake Yi A Sudan Ya Fi Ritsawa Da Fararen Hula Musamman Fadan Da Ake A Cikin Gari

Yakin da ke kara ta’azzara a kasar Sudan ya fi ritsawa da fararen hula musamman a lokacin da ake luguden wuta a yankunan fararen hulan

Yakin da ke kara ta’azzara a kasar Sudan ya fi ritsawa da fararen hula musamman a lokacin da ake luguden wuta a yankunan fararen hulan

Wani sabon rahoto yana bayyana cewa: An gwabza wani kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa a yankuna da dama na babban birnin kasar Khartoum, sannan a karon farko cikin watannin da suka gabata, sojojin Sudan sun samu gagarumin ci gaba a tsakiyar birnin.

Yayin da a birnin Omdurman kuma, Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suke ci gaba da yin luguden wuta kan mai uwa da wabi kan yankin Karari, lamarin da ke janyo mutuwa da jikkatar fararen hula.

Wadanda suka jikkata sakamakon harbin harsasai ana kula da su ne a Asibitin Al-Naw da ke Omdurman, amma wadanda suka jikkata da suka rasa ‘yan uwansu ko kuma suka makale a cikin garin saboda da rashin samun hanyar fita daga cikinsa, suna samun kulawa ne a wani matsugunin da sojojin kasar suka kebance saboda yakin ya ritsa da su kuma suka rasa iyalansu.

Muhammad Al-Fateh, mai kula da cibiyar kula da wadanda suka jikkata da kuma wadanda ba a san ko su waye ba a Sudan ya ce: Suna samun mutane da dama da sukedauke da harsasai a jikkunansu a yankuna daban-daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments