Amurka Ta Roki Isra’ila Ta Rage Zaman Tankiya Da Hezbollah

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya roki ministan tsaron Isra’ila da ke ziyara Yoav Gallant ya kauce wa ci gaba da yaki da kungiyar

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya roki ministan tsaron Isra’ila da ke ziyara Yoav Gallant ya kauce wa ci gaba da yaki da kungiyar Hezbollah ta Lebanon, a yayin da yakin kare-dangin da Isra’ila take yi a Gaza da aka mamaye ke ci gaba, kamar yadda kakakin Ma’aikatar harkokin Wajen Amurka ya bayyana bayan taronsu.

Blinken ya kuma jaddada bukatar daukar matakai na tabbatar da kare ma’aikatan agaji a yankin da aka mamaye.

Blinken “ya jaddada muhimmancin kauce wa karuwar yaki da kuma cim ma mafita ta diflomasiyya wacce za ta bai wa iyalai ‘yan Isra’ila da ‘yan Lebanon damar komawa gidajensu,” a cewar mai magana da yawun Ma’aikatar ta Harkokin Waje Matthew Miller.

Sanarwar ta Miller na zuwa ne a daidai lokacin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi barazanar mamayar sojoji a Lebanon.

‘Yan kwanaki kadan da suka wuce ne, sojojin Isra’ila suka ce “sun amince sun kuma yi nazari” kan shirin mamaye Lebanon, duk da cewa Amurka na yin aiki don hana rikidewar kai hare-hare da aka shafe watanni ana yi kan iyakar kasashen zuwa cikakken yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments