MDD : Kashi 90% Na Yaran Falasdinawa Na Fama Da Tamowa

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa Falasdinawa rabin miliyan a Gaza na fuskantar bala’in yunwa yayin da ake fuskantar barazanar yunwa a

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa Falasdinawa rabin miliyan a Gaza na fuskantar bala’in yunwa yayin da ake fuskantar barazanar yunwa a fadin zirin Gaza sakamakon tsanantar hare-haren da Isra’ila ta yi a makonnin baya-bayan nan.

Sabon rahoton na musamman” daga tsarin sa ido kan yunwa na Majalisar Dinkin Duniya, (IPC), ya ce daya daga cikin biyar na yawan jama’a, sama da 495,000 yanzu suna fuskantar bala’i na matsanancin karancin abinci.

Rahoton ya ce lamarin ya sake tabarbarewa ne sakamakon sabbin matakan soji da Isra’ila ke dauka” wanda ya sanya hadarin yunwa zai ci gaba da wanzuwa a duk fadin zirin Gaza muddin aka ci gaba da samun tashe-tashen hankula da kuma hana kai agajin jin kai.”

Fiye da rabin [gidaje a Gaza sun ba da rahoton cewa, ba su da wani abinci da za su ci a cikin gidan.

Kakakin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu UNRWA, Adnan Abu Hasna, ya bayyana cewa mummunan yanayi a arewacin Gaza ya kai wani intaha, wanda ya bar dubun dubatan iyalai cikin halin yunwa.

Ya kara da cewa 90% na yara a yankin suna fama da rashin abinci mai gina jiki, yana mai kira da a samar da mafita cikin gaggawa don dakatar shawo kan lamarin.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji, yara 50,000 ne ke bukatar kulawa cikin gaggawa saboda rashin abinci mai gina jiki.

Baya ga karancin abinci, dubunnan daruruwan na fuskantar karancin ruwan sha a yankin da aka yi wa kawanya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments