Iran: An Gudanar Da Muhawara Ta 4 Tsakanin Yan Takarar Shugaban Kasa A Zaben Ranar 28 Ga Wannan Yuni

A jiya litinin da yamma ne yan takarar shugaban kasa 6 a zaben shugaban kasar da za’a gudanar a ranar 28 ga watan Yunin da

A jiya litinin da yamma ne yan takarar shugaban kasa 6 a zaben shugaban kasar da za’a gudanar a ranar 28 ga watan Yunin da muke ciki a nan kasar Iran suna gudanar da muhawara na 4  inda ko wane daga cikin yan takarar guda 6 suka bayyana shirinsu dangane da siyasar kasar Iran na harkokin waje.

Yan takarar dai sun hada da Mohammad Baqer Qalibaf, Masoud Pezeshkian, Amir-Hossein Ghazizadeh Hashemi, Alireza Zakani, Mostafa Pour-mohammadi, da kuma Saeed Jalili.

Ga wasu daga cikin ra’ayoyinsu a wannan muhawarar:

Zakani: Kada ku bari kasashen waje su raba tsakaninku da kabilanci, don ba wanda yake da ikon hada mutanen kasar Iran fada a tsakaninsu. 

Jalili: Mafi muhimmanci a sha’anin harkokin wajen shi ne kare hakkin mutanen kasa da kuma samar da dukkan bukatun su daga kasashen waje. Don haka ba wai kawai dole sai an dagewa kasar Iran takunkuman tattalin arziki ba , sai dai kasashen da suka yi hakan sai sun yi nadama.

Pourmohammadi: An sanyamu cikin kangin takunkuman tattalin arziki na kimani shekaru 15, don hakar yarjeniyar JCPAO day ace daga cikin hanyoyin dauke wadannan takunkuman. Zamu jarraba wasu hanyoyin.

Sauran yan takarar sun fadi ra’ayinsu mai kama da wadanda muka ambata. A halin yanzu dai saura muhawara guda wanda yan takarar zasu gudanar kafin zabe a ranar Jumma’a mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments