Tarayyar Afrika Ta Kira Da A Gaggauta Yi Wa Kwamitin Sulhu Na MDD Garambawul 

Kasashen Afrika, sun sake nanata kiran da a gaggauta yi wa kwamitin sulhu na MDD, garabawul. Kwamishinan kula da harkokin siyasa da tsaro da zaman

Kasashen Afrika, sun sake nanata kiran da a gaggauta yi wa kwamitin sulhu na MDD, garabawul.

Kwamishinan kula da harkokin siyasa da tsaro da zaman lafiya na Tarayyar Afrika (AU) ne Bankole Adeoye ya nanata bukatar, yana mai kira da tattaunawa tsakanin kasashen Afrika domin gaggauta hakan.

Kamfanin dillancin labarai na Algeria APS, ya ruwaito Bankole Adeoye na bayyana haka a birnin Algiers na Algeria, yayin wani taron ministoci karo na 11 na kwamitin AU mai shugabannin kasashe da gwamnatoci 10 game da yi wa kwamitin sulhu na MDD garambawul.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen Algeriya Ahmed Attaf ya ce, nahiyar Afrika na son a yi wa kwamitin sulhun garambawul, Yana mai jaddada cewa, wariyar da ake nuna wa Afrika a kwamitin, yana mummunan tasiri ga tsarin harkokin duniya baki daya.

Shi kuwa Timothy Musa Kabba, ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Saliyo, ya yi kira ga shugabannin kasashen su gaggauta tattaunawar da za ta kai ga cimma wannan manufa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments