Zanga-Zangar Adawa Da Yakin Isra’ila Kan Gaza Na Kara Bazuwa A Fadin Amurka

Rahotanni sun ce magoya bayan Falasɗinu da ke fafutikar ganin an kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma goyon bayan

Rahotanni sun ce magoya bayan Falasɗinu da ke fafutikar ganin an kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma goyon bayan da Amurka ke bayarwa, na shirin yin ƙawanya ga Fadar White House ta Amurka a ƙarshen makon nan.

Gamayyar kungiyoyi masu fafutuka irin su CODEPINK da Council on American Islamic Relations a ranar Juma’a sun bayyana cewa an shirya yin zanga-zanga a ranar Asabar, a lokacin da za a cika wata takwas ana yaƙin Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma jefa mutane cikin bala’i da yunwa.

Amurka wadda babbar ƙawar Isra’ila ce, an ta yi mata bore iri-iri a Washington da kuma wurare da ke kusa da White House, zuwa rufe hanyoyi kusa da tashoshin jirgin ƙasa da kwalejoji.

Akalla jami’ai takwas ne suka yi murabus daga gwamnatin shugaba Joe Biden, saboda rashin amincewarsu da manufofinsa. Masu zanga-zangar sun kuma dakile wasu lamuran yakin neman zaben Biden.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments