MDD Ta Saka Isra’ila Cikin Jerin Masu Kashe Kananan Yara A Duniya

Hukumar Palasdinawa ta sanar da cewa,  shigar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin jerin sunayen  masu kisan yara  na Majalisar Dinkin Duniya  mataki ne

Hukumar Palasdinawa ta sanar da cewa,  shigar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin jerin sunayen  masu kisan yara  na Majalisar Dinkin Duniya  mataki ne da ya dace na dorawa wannan gwamnatin hukunci. Wani memba na Hamas ya kuma lura cewa an yi watsi da gwamnatin sahyoniyawan kuma kotunan kasa da kasa suna gurfanar da su gaban kuliya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA  ya habarta cewa, hukumar Palastinu ta dauki shigar Isra’ila cikin wannan  jeri na MDD a matsayin matakin da ya dace na ladabtar da wannan gwamnati tare da jaddada cewa: duniya baki daya ta amince da kasar Palastinu da wadannan ayyuka na ci gaba da kuma kudurorin kasa da kasa sun nuna cewa Isra’ila ta zama saniyar ware a fage na kasa da kasa.

 Wannan hukuma ta bayyana cewa sanya Isra’ila cikin jerin sunayen Majalisar Dinkin Duniya na masu aikata kisan gillar da ake yi wa kananan yara Palasdinu mataki ne da ya dace domin a hukunta wannan gwamnati tare da dakatar da laifukan da take aikatawa.

Har ila yau, Ezzat al-Rashq, mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, a yayin wani taron manema labarai, ya jaddada cewa shigar da sunan gwamnatin sahyoniyawan a cikin bakin jerin  na Majalisar Dinkin Duniya na masu kashe yara, ya fusarta Netanyahu; Sojoji da gwamnatinsa da kuma sojojin yahudawa.

Al-Rashq ya yi nuni da cewa kotunan duniya sun ki amincewa da gwamnatin sahyoniyawa, kamar yadda kuma suka gurfanatr da ita inda a yanzu ake tuhumar tad a aikata kisan kare dangi.

Al-Rashiq ya ce harin bam da ake kaiwa  kan fararen hula Palasdinawa da suka hada da mata da kananan yara yana a matsayin  hujja  kowace fuska, tare da tabbatar da cewa sojojin gwamnatin yahudawa bata yin biyayya ga kururori da dokoki na kasa da kasa.

Gwamnatin yahudawan sahyoniya tana cikin jerin bakar fata na gwamnatocin kashe yara

 A jiya ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sanar da cewa, a karshe Majalisar  ta yanke shawarar sanya Tel Aviv cikin jerin masu aikata laifukan kisan kananan yara a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments