Kasashen Iraki, Kuwait da Saudiyya sun yi maraba da shawarar kasashen Ireland, Norway, da kuma Spain na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa.
Kasashen larawan uku sun fitar da sanarwa daban daban, inda suka bayyana goyon bayansu ga matakin da kasashen Turan suka dauka a baya baya nan na amincewa da kasar Falasdinu.
Ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta ce matakin da suka dauka wani muhimmin mataki ne na farko na maido da ‘yancin al’ummar Palasdinu, tana mai jaddada cewa zaman lafiyar yankin ya dogara ne kan samar da kasar Falasdinu mai al-Quds a matsayin babban birninta.
Ita ma ma’aikatar harkokin wajen Kuwait ta yaba da matakan wadanda ta ce za su taimaka wajen aiwatar da kudurorin kasa da kasa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma shirin zaman lafiya na kasashen Larabawa na shekarar 2002.
Saudiyya ta fada a ranar Laraba cewa ta yi maraba da shawarar da Norway, Spain, da Ireland suka dauka na amincewa da kasar Falasdinu.
Masarautar Saudiyya ta ce ta yaba da matakin “wanda ke tabbatar da amincewar kasa da kasa kan hakki na al’ummar Falasdinu na cin gashin kai,” a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.
Riyadh ta kuma bukaci kasashe da su dauki wannan matsayi, “wanda zai taimaka wajen samar da amintacciyar hanyar zaman lafiya mai dorewa.
Sanarwar ta kara da cewa, wadannan kudurori na da nufin baiwa al’ummar Palasdinu damar yin amfani da ‘yancin cin gashin kansu da kuma kafa kasa mai cin gashin kanta a kan iyakokin shekarar 1967, wadda gabashin Quds ya zama babban birninta.