Amurka Ta Bukaci Tattaunawa Da Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta bukaci tattaunawa da Iran kan yakin da take fafatwa da ita, sai

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta bukaci tattaunawa da Iran kan yakin da take fafatwa da ita, sai dai, inji shi, Iran ta rika ta bayyana matsayinta, abinda ya rage shi ne Amurka ta aiwatar da su.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar  Iran ya nakalto Aragchi yana fadawa tashar talabijan ta Aljazeera na kasar Katar kan cewa, sun tattaunawa wasikar da mataimakin shugaban kasar Amurka JD vance ya aikawa kasar, kuma sun ga ba bu bukatar wata tattaunawa da jami’an gwamnatin Amurka ko kuma wani wakilinsu danga ne da yakin. Ya kra da cewa jita jitan da wasu kafafen yada labarai suke fada kan cewa za’a sake haduwa da tsakanin Iran da Amurka a wata tattaunawa ba gaskiyane ba.

Yace Iran ta rika ta bayyana matsayinta da kuma sharuddanta, don haka idan Amurka tana son zaman lafiya ta aiwatar da su, idan ba haka ba, iran a shirye ta ke ta fuskanci Amurka a duk abinda ta shirya.

Ya ce batun sake haduwa da jami’an gwamnatin Amurka kai tsaye ko tare da masu shiga tsakani shi ne, matakan da Amurka ta dauka na aiwatar da sharuddanta.

Sharuddan Iran sun hada da dauke dukkan takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran, sakin kudadenta da aka sace, ko aka hana tabasu, dauke dukkan sojojin Amurka daga yankin. Da kuma kawo karshen yaki a dukkan fagagen fama da kawayen kasar. Kasashen Qatar da Pakistan sun isar da sakon ga Amurka. Kuma muna godiya.

Dangane da Hurmuz yace, Iran tana bukatar sabon doka ta kasa da kasa wacce zata tabbatar da mashigar ruwa a matsayin mallakin Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted