Chadi : Babbar Jam’iyyar Adawa Ta Gabatar Da Korafi Kan Zaben Kasar

Kwanaki biyu bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Chadi, babbar jam’iyyar hamayya ta kasar ta mika bukatar ta ga majalisar tsarin mulkin kasar

Kwanaki biyu bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Chadi, babbar jam’iyyar hamayya ta kasar ta mika bukatar ta ga majalisar tsarin mulkin kasar inda take korafi game da sakamakon zaben da shugaban kasar na rikon kwarya Mahamat Idriss Deby ya samu.

Jam’iyyar Masra Success ta ce ta lashe zaben shugaban kasa da kashi 73% na kuri’un da aka kada, bisa ga kididdigar da ta yi, amma ba tare da fitar da cikakken bayani ba.

Mataimakin shugaban jam’iyyar, Sitack Yombatina Béni, ya bayyana irin kura-kuran da aka samu a lokacin kada kuri’ar, musamman hana shiga rumfunan zabe da hana gudanar da kidayar kuri’u, da rashin kayan zabe, da akwatunan zabe da sojoji suka kwashe.

Ya kara da cewa hukumar zabe ta kasa ta hana shi gudanar da aikin, wanda ya saba wa sashi na 89 na kundin tsarin zabe.

A karshen makon jiya Hukumar zaben kasar ta Chadi ta bayyana cewa shugaban kasar na rikon kwarya Mahamat Idriss Deby Itno ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu da sama da kashi 61% na jimillar kuri’un da aka kada.

Shi kuwa babban abokin hamayyarsa kana Firaministansa, Succes Masra, ya samu kashi 18.53% na kuri’un.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments