Masu hannu da shuni sun yi alkawarin samar da sama da dala Biliyan biyu don taimakawa zirin Gaza.
A yayin taron da aka gudanar na masu ba da agaji na kasa da kasa a Kuwait, mahalarta taron sun yi alkawarin samar da wadanan kudaden don taimakawa Gaza.
Taron wanda kungiyar agaji ta Islama ta kasa da kasa (IICO) da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (Ocha) suka shirya, ya tanadi cewa za a raba kudaden ne tsawon shekaru biyu, tare da yiyuwar tsawaitawa, da nufin tallafawa ayyukan jin kai masu muhimmanci a cikin yankin Falasdinawa da aka yiwa kawanya.
Yakin da Isra’ila ta kadammar kan Gaza, bayan harin ba zata da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba ya lalata zirin Gaza gabadayansa.
Yakin ya yi sanadin mutuwar falasdinawa kimanin 35,000 wadanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata, sannan sama da mutum dubu 78 da rabi ne suka jikkata.