Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun bayyana cewa akalla falasdinawa 6 sun yi shahada yayin da wasu guda 20 kuma suka jikkata a wani hari da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suke yi da aka cimma tsakani
A harin farko falasdinawa 2 ne suka yi shahada bayan da jirgin sama mara matuki na HKI ya kai hari kan wata mota a titin Al-rashid dake khan yunis a kudancin gaza a jiya litinin, yayin da wasu guda biyu kuma na daban sun yi shahada ne a harin da aka kai a yankin al-mawasi dake kusa da khan yunis.
kungiyar masu kama kifi ta falasdinu ta bayyana cewa akwai wasu falasdinawa guda 3 da suka jikkata bayan da jirgin sama mara matuki ya kai musu a hari a bakin teku da zirin gaza, kuma ya kashe bafalasdine guda duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka sanya wa hannu a watan oktoba da kasar Amurka ta shiga tsakani
kididdigar baya bayan nan da aka fitar ta nuna cewa adadin mutane da aka kashe a yakin kare dangi da isra’ila ta kaddamar kan alummar Gaza tun a watan oktoban shekara ta 2023 ya kai mutane 73098 yayin da 173571 kuma suka jikkata,
yanzu haka dai majalisar dinkin duniya ta bukaci a gudanar da wani zaman a musamman domin tattaunawa kan yadda zaa kawo karshen ci gaba da kisan kare dangi da HKI ke yi a yankin gaza da ya sabama dan adamtaka