Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare.
Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin.
A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta ci gaba da bai wa Majalisar Dinkin Duniyar hadin kai domin kyautata rayuwar al’ummar kasar ta Yemen da kuma shimfida zaman lafiya.
A wani labari mai alaka da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta amabci cewa za a yi ganawa a tsakanin minista Abbas Arakci da takwaransa na Faransa Jean Noel Baro a gobe Laraba 26/ Nuwamba a birnin Paris.
Jigon tattaunawar shi ne bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma batun furusunonin Faransa da suke a Iran.
Haka nan kuma tattaunawar bangarorin biyu za ta tabo halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, sai kuma Shirin Iran na makamashin Nukiliya.