Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Lebanon ta sanar da shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani sanadiyyar harin da HKI ta kai wa wata mota a

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Lebanon ta sanar da shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani sanadiyyar harin da HKI ta kai wa wata mota a garin Zudhar dake gundumar Nabadhiyya.

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da laabrin cewa a jiya  Juma’a sojojin HKI sun bude wuta a cikin Lebanon daga kan iyakar ‘alhamamis”. Bude wutar da manyan bindigogi ya kuma shafi kudancin birnin al-khayam.

Har ila yau birnin na alkhayam ya fuskanci wasu hare-hare daga HKI da ta yi amfani da jiragen sama marasa matuki.

HKI tana ci gaba da keta tsagaita wutar yaki da aka yi tun a 27 ga watan Aprilu 2024.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted