Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domin  Kare Kanta

Shugaba kasar Venezuela Nicolas Maduro ne ya bayyana cewa, kasarsa ta mallaki makamai masu linzami samfurin “Igla-S” kirar kasar Rasha har 5000, domin tabbatar da

Shugaba kasar Venezuela Nicolas Maduro ne ya bayyana cewa, kasarsa ta mallaki makamai masu linzami samfurin “Igla-S” kirar kasar Rasha har 5000, domin tabbatar da tsaronta.

Shugaba Maduro ya ce, tuni an girke wadannan makaman a wurare masu muhimmanci, kuma za a sake girke su a fadin kasar domin bayar da kariya ga sararin samaniyar kasar.

Bugu da kari shugaban kasar taVeneuela ya ambaci cewa da akwai dubban kwararru da su ka iya sarrafa wadannan makaman na tsaron sararin samaniyar kasar, da za su iya watsuwa a duk inda aka girke makaman a cikin dukkanin kusurwowi hudu.
Nicholas Maduro ya kuma ce, wajibi kasar Venezuela ta zama mai kariya, ta yadda babu wanda zai iya kawo mana hari, domin ba mu kai wa kowace kasa hari ba.”

Acikin kwanakin bayan nan dai Amurka ta bude tsokanar kasar Venezuela, ta yadda take kai wa jiragen ruwanta hare-hare bisa riya cewa suna dauke da muggan makamai zuwa Amurka.

Kasar Venezuela da sauran kasashen yankin Carriebia sun yi tir da halin tsokanar na Amurka.

A can kasar Rasha ma’aikatar harkokin waje ta yi suka akan kai da komowar sojojin Amurka a cikin yankin Carrebia tana mai jaddada goyon bayanta ga kasar Venezuela, sannan kuma ta bukaci Amrukan da ta kaucewa duk wani abu da zai kai ga yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted