Masani Kan Harkokin Tsaro Ya Ce: Makami Mai Linzamin Iran Kirar Ghadir Ya Aike Da Sako Ga Isra’ila

Makami mai linzami na Iran kirar “Ghadr-H” ya aika da sako mai muni ga gwamnatin mamayar Isra’ila Wani masani kan harkokin tsaro da tsare-tsare Kanar

Makami mai linzami na Iran kirar “Ghadr-H” ya aika da sako mai muni ga gwamnatin mamayar Isra’ila

Wani masani kan harkokin tsaro da tsare-tsare Kanar Abdul Karim Khalaf ya bayyana cikakkun bayanai masu inganci da siffofi na musamman na makami mai linzamin na Iran “Ghadr H”, yana mai jaddada cewa; Makamin ya aike da sako mai karfi ga gwamnatin mamayar Isra’ila saboda karfin da take da shi na kutsawa cikin mafi tsauri na tsaron iska da kuma gujewa radar.

Khalaf ya bayyana a cikin bayanansa cewa: “Ghadr” ya bambanta da sauran hasken wadda da ba a taba ganin irinsa ba a cikin yaki da kuma karfin da yake da shi na barna saboda fasahar da ke dauke da shi na musamman, baya ga gudun kilomita 10,000 a cikin sa’a guda.

Masanin tsaro ya bayyana cewa: Makami mai linzamin na “Ghadr” wani ci gaba ne na makami mai linzami na “Shahab 3” kuma yana cikin wani sabon ci gaban zamani ne na makamai masu linzami. Siffar sa ta musamman ta ta’allaka ne a cikin hasken kan yakinta mai nauyin fiye da kilogiram 650, duk kuwa da cewa makami mai linzamin na da girma sosai, wanda nauyinsa ya haura tan 15.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted