Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru,
Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa.
Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan dake suke gudun hijira a kasar iran , yace iran ta taimaka musu sosai duk da matsayin lamba da take fuskanta daga kasashen turai, inda ta kakaba mata mummuna takunkumin zalunci.
Iran ta karbi yan gudun hijira akalla miliyan 3.8 daga kasashe daban daban wanda mafi yawancinsu yan kasar Afghanistan ne,