Janar Safawi; Iran Ta Kashe Matukan Jirgin Saman Isra’ila 16 A Yakin Kwanaki 12 Da Aka Yi A Tsakaninsu

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Janar Safawi ya bayyana cewa: An kashe matukan jirgin saman yakin Isra’ila 16 a harin

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Janar Safawi ya bayyana cewa: An kashe matukan jirgin saman yakin Isra’ila 16 a harin da aka kaddamar kan Iran

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Yahya Rahim Safawi ya sanar da cewa: Iran ta harba makamai masu linzami sama da 500 kan haramtacciyar kasar Isra’ila a lokacin yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. Ya tabbatar da cewa: An yi nasarar kashe matukan jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila akalla 16 a daya daga cikin hare-haren makamai masu linzami da aka kai kan cibiyar horar da matukan jirgi.

Wannan ya zo ne a cikin jawabin da Manjo Janar Yahya Rahim Safavi ya gabatar a yammacin ranar Litinin a wajen bikin tunawa da makon tsaro mai alfarma daga shekara (1980 zuwa 1988) a zauren Sheikh Mufid da ke Jami’ar Qum. Ya bayyana muhimmancin jami’o’i da matasa masu tasowa, inda ya ce, “Baya ga matsayinsu na ilimi da fasaha, jami’o’i za su iya zama makasudin bunkasa al’amuran da suka dace, masu ilimi, da kirkire-kirkire masu iya fuskantar barazanar ciki da waje.

Ya ci gaba da cewa: “Ta hanyar yin amfani da bincike, kirkire-kirkire, da fasahar kimiyya da al’adu, matasa za su samu karfin tafiyar da al’amuran kasa da na shiyya da kuma karfafa hadin kan kasa da hadin kai tsakanin gwamnati da al’ummar kasa.”

Ya jaddada cewa, wadannan iyakoki suna taka muhimmiyar rawa ba kawai a fannin ilimi ba, har ma da bunkasa dabarun tattalin arziki, siyasa da zamantakewar kasar su da kuma karfafa tushen tsaro da mulkin kasa.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted