Iran da Rasha sun cimma yarjejeniyar $ biliyan 25 don gina tashoshin makamashin nukiliya

Kasashen Iran da Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dala biliyan 25 don gina tashoshin makamashin nukiliya guda hudu a wani bangare na yarjejeniyar

Kasashen Iran da Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dala biliyan 25 don gina tashoshin makamashin nukiliya guda hudu a wani bangare na yarjejeniyar hadin gwiwa ta dogon lokaci da nufin karfafa alaka tsakanin Tehran da Moscow a fannoni daban-daban.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar zartarwa a birnin Moscow yau Juma’a tsakanin Kamfanin Hormoz na Iran da kamfanin Rosatom Project na kasar Rasha don ginawa da kuma kafa cibiyoyin samar da makamashin nukiliya na zamani hudu a garin Sirik da ke gabar teku a lardin Hormozgan na kudancin kasar.

Babban aikin da za a gudanar a gundumar Kuhestak na yankin Sirik na lardin Hormozgan, zai iya samar da megawatts 5,020 daga makamashin nukiliya.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin kasashen biyu wato Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tarayyar Rasha, domin bunkasa hadin gwiwa ta hanyar amfani da makamashin nukiliya cikin lumana.

Da yake karin haske kan shirin Iran na samar da megawatts na wutar lantarki mai karfin megawatt 20,000 ta hanyar bunkasa tashoshin samar da makamashin nukiliya, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran AEOI ya shaidawa manema labarai cewa, a halin yanzu kasar Rasha na ci gaba da aikin gina rukunin na biyu da na uku na tashar nukiliyar Bushehr.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted