Shugaban Kasar Faransa Zai Amince Da Kasar Falasdinu A Ranar Litinin Mai Zuwa A Birnin New York

Shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa; Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York Shugaban kasar Faransa Emmanuel

Shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa; Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar a yammacin jiya Juma’a cewa: Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York.

Macron ya bayyana cewa: Amincewa da kasar Falasdinu wani bangare ne na cikakken shirin zaman lafiya da ke tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga Isra’ila da Falasdinu.

Emmanuel Macron zai gabatar da jawabi don tabbatar da wannan karramawa a ranar litinin da misalin karfe 3:00 na rana a birnin New York (9:00 na yamma agogon Paris), yayin wani taron da zai jagoranta tare da yarima mai jiran gado na Saudiyya.

Fadar Elysée ta ce: “A cewar sabon bayanan da aka samu, Mohammed bin Salman zai yi magana ta hanyar taron bidiyo.”

A cikin wannan mahallin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Pascal Confavro ya bayyana a ranar Juma’a cewa; “Wannan amincewa ba ya wakiltar ƙarshen kokarin diflomasiyya … kuma ba furuci ne na alama ba, amma a maimakon haka wani bangare ne na hangen nesa mai zurfi kuma mafi mahimmanci.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted