Iran Ta Bukaci Kwamitin Tsaro Na MDD Ta Zabi Diblomasiyya Kan Fito Na Fito

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya shiga tsakaninta da kasashen turai guda 3 don tabbatar da

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya shiga tsakaninta da kasashen turai guda 3 don tabbatar da cewa sun zabi diblomasiyya da Iran mai makon fito na fito da ita.

Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa Iran ta gabatar masu da hanyoyin warware matsaloli tsakaninsu da JMI kuma masu yiyuwa, amma da alamun sun fi son fito na fitoda JMI, dangane da tsarin nan na Snapback dangane da yarjeniyar Nukliya ta JCPOA ta shekara ta 2015.

 Aracgchi ya bayyana haka ne jim kadan kafin kwamitin yafara zama don tattauna batun tsarin na tsapback a jiya alhamis .

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted