Hamas Tana Maraba Da Duk Wata Shawarar Da Zata Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci Kan Gaza

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falasdinu Kungiyar gwagwarmayar Musulunci

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falasdinu

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Lahadin da ta gabata cewa, tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen yunkurin da ake yi na dakatar da kai hare-hare kan al’ummar Falasdinu, tana mai bayanin cewa ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma matsaya.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar ta ce: “Ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta. A wannan karon, kungiyar Hamas na maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a kokarin da ake na dakatar da wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu.”

Sanarwar ta kara da cewa: Kungiyar Hamas ta tabbatar da cewa a shirye take ta zauna kan teburin tattaunawa nan take, don tattaunawa kan batun sakin fursunonin da za a yi a musayar yawu da bayyana kawo karshen yakin, da ficewar sojojin mamayar Isra’ila daga zirin Gaza gaba daya, da kuma kafa wani kwamitin da zai tafiyar da yankin na Gaza daga Falasdinawa masu cin gashin kai, wanda zai fara aikinsa nan take.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted