Rundunar sojin Yeme ta sanar da kai hare-hare guda 8 da jirage sama marasa matuka ciki kan muhimman wurare a Isra’ila
Dakarun sojin Yemen sun sanar da yammacin jiya cewa, sun kai wasu manya-manyan farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen saman yaki marasa matuka ciki guda takwas a kan wasu wurare da dama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye. An kai hare-haren ne kan filin jirgin saman Ramon da muhimman wurare da na sojoji da suka hada da Negev, Umm al-Rashrash, Ashkelon, Ashdod, da Jaffa.
Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmayarsu masoya, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan ‘yan uwa a zirin Gaza, da kuma tabbatar da gwagwarmayar kasar Yemen a fagen yaki da jihadi mai tsarki, bangaren sojin saman Yemen ya kaddamar da hare-hare da wasu jirage marasa matuka kan yankunan Negev, Umm al-Rashrash, Ashkelon, Ashdod, da Jaffa.
Dakarun kasar Yemen sun tabbatar da cewa: Za su kara kai hare-haren soji, kuma ba za su ja da baya daga goyon bayan da suke baiwa Gaza ba, ba tare da la’akari da sakamakon da zai biyo baya ba. Yemen cikin yardar Allah tana kera makamanta domin samun gagarumin tasiri da ingancin ayyukanta.